Home Labaru Hare-Hare: An Kashe Mutane 349 Cikin Wata Guda A Nijeriya — Rahoto

Hare-Hare: An Kashe Mutane 349 Cikin Wata Guda A Nijeriya — Rahoto

364
0
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Uku A Jihar Katsina

Akalla mutane 349 aka kashe sakamakon munanan hare-haren da aka kaddamar a cikin watan Nuwamban da ya gabata a sassan Nijeriya kamar yadda wani rahoton kungiyar ‘Nigeria Mourns’ ta fitar ke cewa.

Rahoton ya yi nazari a kan kashe-kashen da aka samu a sassan Nijeriya cikin watan Nuwamba kadai, kuma kingiyar ta tattara alkaluman ta ne daga jaridu da majiyoyin iyalan mamatan, bayan ta kewaya jihohin Nijeriya 23.

Haka kuma, Rahoton ya nuna cewa, fararen hula 309 aka kashe daga cikin adadin, yayin da aka hallaka jami’an tsaro 40, sannan  an yi garkuwa da mutane 290 a cikin watan. Jihar Borno ke kan gaba wajen yawan asarar rayukan al’umma a cikin watan kamar yadda alkaluman mamatan su ka nuna.

Leave a Reply