Home Labaru Zaben Kogi: ‘Yan Takara Biyar Na PDP Sun Janye Wa Idris Wada

Zaben Kogi: ‘Yan Takara Biyar Na PDP Sun Janye Wa Idris Wada

376
0
Yan Takara Biyar Na Pdp Sun Janye Wa Idris Wada
Yan Takara Biyar Na Pdp Sun Janye Wa Idris Wada

A ci-gaba da shirye-shiryen zaben fidda dan takarar gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar PDP, ‘yan takara biyar daga cikin 16 da ke neman tikitin takara a zaben gwamna mai zuwa ne su ka janye wa tsohon gwamnan jihar Idris Wada.

Idris Wada dai shi ne gwamnan da jam’iyyar APC ta kada a zaben gwamna da aka yi shekaru hudu da su ka gabata.

‘Yan takarar da su ka janye ma shi kuwa sun hada da Salihu Atawodi da Muhammed Tetes, da Emmanuel Omebije, da Grace Iye Adejor da da kuma Victor Adoji.

Idan dai ba a manta ba, Jam’iyyar PDP ta ce idan har akwai abin da ya ke yi mata dadi game da zaben jihar Kogi ba zai wuce yadda APC ta tsaida Yahaya Bello a matsayin dan takarar ta ba.