Home Labaru Matakan Tsaro: Za Mu Sama Wa ‘Yan Afrika Ta Kudu Tsaro A...

Matakan Tsaro: Za Mu Sama Wa ‘Yan Afrika Ta Kudu Tsaro A Abuja – Minista

434
0
Mohammed Bello, Ministan birnin Tarayya Abuja
Mohammed Bello, Ministan birnin Tarayya Abuja

Ministan birnin Tarayya Abuja Mohammed Bello, ya yi kira ga al’ummomin Abuja su yi hakuri bisa abubuwan da su ka faru a kasar Afrika ta kudu, sannan kada su afka wa kamfanonin ‘yan kasar.

Karanta Wannan: Matakan Tsaro: Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kama Kayan Hada Bom A Birnin Abuja

Ya ce ‘yan Kasar Afrika Ta kudu da ke zama a Abuja su cigaba da zamn su, ya na mai cewa gwamnati za ta sama masu kariya yadda ya kamata.

Ministan, ya kuma roki matasa da sauran mutane su yi hakuri, su daina farautar kamfanonin ‘yan kasar Afrika ta Kudu, cewa da yawa daga ciki duk hadin gwiwa ne da attajiran Nijeriya.

Ya ce idan aka cigaba da haka, lamarin zai durkusar da tattalin arzikin kasa, ganin cewa mutane da dama su na aiki a kamfanonin kuma duk ‘yan Nijeriya ne.

Minista Bello ya kara da cewa, an aika da jami’an tsaro da dama domin samar da tsaro a wadannan wurare.