Home Labaru Ramuwar-Gayya: Kamfanin MTN Ya Rufe Ofisoshin Sa Gaba Daya A Nijeriya

Ramuwar-Gayya: Kamfanin MTN Ya Rufe Ofisoshin Sa Gaba Daya A Nijeriya

666
0
MTN
MTN

Hukumar kamfanin sadarwa na MTN, ta sanar da garkame dukkan kamfanoninta da ofisoshin ta har sai abin da hali ya yi, sakamakon hare-haren ramuwar gayya da wasu ‘yan Nijeriya su ka fara kai mata, biyo bayan cin zarafi tare da kashe ‘yan Nijeriya da ake yi a kasar Afirka ta kudu.

Karanta wanna: Martani: Kungiyar Dalibai Ta Najeriya Tarufe Kamfanin Mtn A Kaduna

Wata majiya ta ce, kamfanin MTN ya sanar da rufe ofisoshin ne, sakamakon an fara kai mata hari a wasu jahohin Nijeriya, inda har ta kai ga an kona mata ofisoshi.

Wannan dai shi ne karo na farko da ‘yan Nijeriya ke ramuwar gayyar abin da ‘yan kasar Afirka ta kudu ke yi wa baki a kasar su, inda a wannan karon sun kashe baki ‘yan Afirka da dama.

 A cewar kamfanin MTN, a kwanan da ya gabata, an kai wa ofisoshin su hari da ma abokan huldar su, a matsayin harin ramuwar gayyar abin da ke faruwa a kasar Afirka ta kudu na harin kyamatar baki ‘yan Afirka.

Kamfanin ya cigaba da cewa,  su na da niyyar ci-gaba da aikin su na gamsar da abokan huldar su, amma ba su da tabbacin tsaron ma’aikatan su da abokan huldar su, don haka sun kulle duk wasu ofisohin su har sai abin da Allah ya yi.