Home Labaru Zaben Kano: Kotu Ta Aike Wa INEC Da Kwamishinan ‘Yan Sanda Sammaci

Zaben Kano: Kotu Ta Aike Wa INEC Da Kwamishinan ‘Yan Sanda Sammaci

630
0

A yayin da ake ci gaba da sauraron karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta na  Abba Kabir Yusuf, ya shigar a kotun sauraron karar zabe na jihar Kano, kotu ta aike wa kwashinan ‘yan sanda da hukumar zabe ta INEC sammaci.

Karanta Wannan: Rikici: Mutane 11 Sun Mutu A Taraba Da Benue Sakamakon Rikicin Kabilanci

Kotun ta aike wa kwamishinan ‘yan sandan Jihar takardan gayyata domin ya zo kotun ya gabatar da wasu takardu da wadanda suka shigar da karar ke bukata.

Kazalika, an kuma aike wa hukumar INEC takardan gayyata domin gurfana gaban kotun domin bayar da shaidan baki da za ayi amfani da shi yayin sauraron shari’ar.

Sai dai, wakilci kwamishinan ‘yan sandan Sunday Ekwe da ya tafi gudanar da aiki a wani wurin ya bukaci kotu ta bashi lokaci domin gabatar da bayannan da ake bukata daga gare shi.

Alkaliyar kotun, mai shari’a Halima Muhammad ta ba kwamishinan ‘yan sandan kwanaki biyar domin gabatar da bayyanan da ake bukata daga hannunsa yayin da ta ba INEC damar gabatar da shaida a rubuce.

Masu shigar da karar sun bukaci INEC ta ba su damar sauya wasu daga cikin shaidun su kamar yadda kotun daukaka kara da ke zamanta a Kaduna ta amince musu, amma lauyoyin INEC da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da APC sun bukaci a ba su mako guda domin bayar da ba’asi kamar yadda sashi na 47(4) na dokar zabe ya bayar da iko.