Home Labaru Zaben Kananan Hukumomi: Jam’iyyar PDP A Kano Ta Kaurace

Zaben Kananan Hukumomi: Jam’iyyar PDP A Kano Ta Kaurace

147
0

Jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar Kano ta ce ba za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da aka shirya gudanarwa a watan Janairu mai zuwa a jihar ba.

Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar PDPn a jihar Danladi Kagara, ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai.

Wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito na cewa Danladi Kagara, ya ce sun dauki matakin kauracewa zaben ne saboda alamun ba za a yi musu adalci ba.

Za a gudanar da zaɓen ne ranar Asabar 16 ga watan Janairu, inda ake sa ran za a zaɓi shugabannin kananaa hukumomi 44 a jihar.

Gwamnatin jihar dai tace ta ware fiye da naira biliyan biyu domin gudanar da zaɓen.