Home Labaru Murkushe Boko Haram: Zulum Ya Mikawa Gwamnatin Najeriya Bukatu 6

Murkushe Boko Haram: Zulum Ya Mikawa Gwamnatin Najeriya Bukatu 6

186
0

Gwamnan Jihar Barno Babagana Umara Zulum, ya gabatar da wasu bukatu 6 ga tawagar gwamnatin tarayya da ta kai masa ziyarar jaje, inda ya ce a kwai bukatar dauko sojojin haya daga kasashen ketare domin murkushe mayakan boko haram da suka addabi jihar sa.

Zulum ya gabatar da bukatun ne lokacin da ya karbi tawagar gwamnatin a karkashin shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, wadanda suka je jajantawa jama’a kan kisan gillar da mayakan boko haram suka yiwa wasu manoma.

Daga cikin bukatun na Zulum akwai dibar matasan yankin cikin aikin soji da sauran hukumomin tsaro da karfafa hadin kai tsakanin Najeriya da hukumomin Chadi da Kamaru da Nijar domin karkade lungunar da mayakan suke makalewa, sannan kuma da ba sojoji da ‘yan sandan Najeriya motoci masu sulke da ingantattun kayan aiki domin shawo kan matsalar.

Gwamnan ya kuma bukaci taimakon gwamnati wajen kwaso ‘yan Jihar da suka nemi mafaka a kasashen Nijar da Kamaru, kana da sake gina hanyoyin Jihar da suka lalace sakamakon rikicin boko haram da aka kwashe shekaru 11 ana yi.

Idan dai ba a manta ba da lokacin mulkin shugaban kasa Goodluck Jonathan, Najeriya ta yi hayar wadansu sojojin haya daga Afirka ta kudu, wadanda aka rika amfani da su ana yakar Boko Haram, wanda Zulum, yake ganain ya kamata a sake gwadawa.