Home Labaru Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Kaduna Ya Ce Bai Damu Ba Don Ya...

Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnan Kaduna Ya Ce Bai Damu Ba Don Ya Faɗi Zaɓe A Mazaɓar Sa

26
0

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana cewa rashin cin zaɓe da jam’iyyar APC ta yi ba a mazaɓarsa yayin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar alama ce ta cewa an gudanar da zaɓen gaskiya da adalci.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata hira da BBC inda ya ce barin da aka yi mutane suka zaɓi abin da suke so dimokraɗiyya ta fi aiki.

A makon da ya gabata ne dai Jam’iyyar APC ta yi rashin nasara a mazaɓar Gwamna El-Rufai da ke Unguwar Sarki inda jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe zaɓen da ƙuri’a 159 a kujerar kantoma inda APC ta samu ƙuri’u 62.

Hakazalika PDP ta samu ƙuri’u 100 sai kuma APC ta samu 62 a zaɓen kansila a mazabar ta El Rufai.

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa “Yadda mutane suka yi ta murnar cewa mazaɓata inda nake jefa ƙuri’a PDP ta ci mazaɓar ya nuna cewa mu ba mu da murɗiyar zaɓe, ba mu da rashin gaskiya kuma muna barin mutane su zaɓi abin da suke so.

Gwamnan ya bayyana cewa zaɓen da aka gudanar ba zaɓen shi bane domin a cewarsa ” Ni ba na takara, na gama takarata a jihar Kaduna Insha Allahu, mutane suna jefa wa mutanen da suka sani ne ƙuri’a ba wai Nasiru El Rufai ke takara ba.