Home Labaru Toshe Hanyoyin Sadarwa: Al’Ummar Arewa Maso Yamma Sun Yi Na’Am

Toshe Hanyoyin Sadarwa: Al’Ummar Arewa Maso Yamma Sun Yi Na’Am

16
0
SADARWAA

Al’ummar jihohin Kebbi, Sokoto da Katsina sun bayyana cewa a shirye su ke su jure duk wata takura da ƙunci da matsin da za su shiga sakamakon kulle lambobin wayoyin sadarwa da aka yi a Jihar Zamfara, matsawar dai yin hakan zai kakkaɓe masu ‘yan bindiga a yankunan su.

Sun ce takurawar da su ke fuskanta da zaman ƙunci dama tilas ya faru idan aka kai ga kulle layukan wstoyini, amma har gara su fuskanci wannan ƙuncin idan dai za a kawar da ‘yan bindiga sanadiyyar ɗaukar tsatstsauran matakin.

Da yawa ma daga cikin su su na nuna haushi ganin yadda wasu ke ƙorafe-ƙorafe da kuma nuna damuwar su a kan kulle layukan wayoyin da Gwamnatin Tarayya ta yi a yankunan na su.

Sun ce bai kamata a riƙa ƙorafi ba, domin matakin dai an ɗauke shi ne don a kare rayukan al’ummar yankin.

Sun ce dama an ce ‘magani ɗaci gare shi, amma kuma warakar da ya ke samarwa ta fi ɗacin daɗi nesa ba kusa ba.