Home Labaru Yajin Aikin: Shugaba Buhari Ya Roki Likitoci Da Su Koma Bakin Ai

Yajin Aikin: Shugaba Buhari Ya Roki Likitoci Da Su Koma Bakin Ai

11
0
Nigerian Doctors Vow To Continue Strike
Nigerian Doctors Vow To Continue Strike

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki likitocin kasar dake yajin aiki da su yiwa Allah su koma bakin aikin su domin ci gaba da tattaunawa da jami’an gwamnati domin shawo kan matsalolin da suka addabe su.

Yayin ganawa da shugabannin kungiyar likitoci na kasa, shugaban ya kuma roki sauran ma’aikatan lafiya dake shirin tsunduma cikin yakin aikin da su sake tunani akai, inda ya bayyana cewar kasar na matukar bukatar aikin su a wannan lokaci fiye da lokacin da ya shude.

Buhari yace dogon lokacin da ake dauka ana tattauna ya zarce fadawa cikin yajin aiki saboda illar da hakan ke yiwa jama’ar kasa.

Shugaban kasar yace rayukan mutanen dake salwanta lokacin yajin aikin likitocin na da matukar tasiri, saboda haka rungumar hanyar tattaunawa tafi shiga yajin aikin.

Buhari yace a shirye yake ya biya daukacin basussukan da ake bin likitocin da zaran an kammala tantance su, inda ya kara da cewar yajin aikin na su a wannan lokaci ba abinda ya dace ba ne.