Home Labaru Zaben Kamaru: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Kula Da Labaran Da Za...

Zaben Kamaru: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Kula Da Labaran Da Za Su Yada

438
0
Zaben Kamaru: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Kula Da Labaran Da Za Su Yada
Zaben Kamaru: An Bukaci ‘Yan Jarida Su Kula Da Labaran Da Za Su Yada

Hukumomi a jamhuriyyar Kamaru sun kara jan hankulan manema labarai game da irin labarun da suke yadawa kan yakin neman zabe, a lokacin da ake dab da fara zaben kasar.

Wadannan kiraye-kiraye na hukumomi na zuwa ne a lokacin da kungiyar masu fafutuka da ke yunkurin kafa kasar Ambazoniya, ke barazana a kan yiyuwar zabukan.

Har ila yau, akwai wasu jam’iyyun siyasa da hukumomi ke cewa manufar su ita ce su rinjayi magoya bayan su kada su fita su kada kuri’a a zaben.

Sai dai tuni manema labarai suka fara kokawa kan yunkurin sanya takunkumi da hukumar kula da harkokin sadarwa take da nufin yi.