Home Labaru Siyasar Kano: Ganduje Ya Soki Kwankwaso

Siyasar Kano: Ganduje Ya Soki Kwankwaso

393
0
Siyasar Kano: Ganduje Ya Soki Kwankwaso
Siyasar Kano: Ganduje Ya Soki Kwankwaso

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin dan siyasa mara alkibla wanda ba shi da tsari.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abba Anwar ya aike wa manema labarai kan taron Ganduje, ya ce ko a lokacin da Kwankwaso, yake mulki, idan ka duba irin ayyukan ci gaban da ya samar da sauran tsare-tsaren sa, za ka gane cewa bai san inda ya dosa ba a matsayin sa na shugaba.

Sai dai wasu na ganin wadannan zarge-zargen na gwamnan tamkar martani ne kan wani faifen bidiyo da aka ga Kwankwason na jawabi bayan hukuncin kotun koli, inda yake tsinuwa ga zargin zaluncin da ya ce an yi musu.

Tun bayan da kotun kolin Najeriya ta tabbatar wa Ganduje, nasarar sa ne dai gwamnan ya mika goron gayyata ga ‘yan hamayya kan su zo su hadu don ciyar da jihar Kano gaba.