Home Labaru Hukunci: Kotu Ta Hana Yi Wa Musulmin Rohingya Kisan Kare-Dangi

Hukunci: Kotu Ta Hana Yi Wa Musulmin Rohingya Kisan Kare-Dangi

492
0
Hukunci: Kotu Ta Hana Yi Wa Musulmin Rohingya Kisan Kare-Dangi
Hukunci: Kotu Ta Hana Yi Wa Musulmin Rohingya Kisan Kare-Dangi

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar da umarnin daukar matakan kare Musulman Rohingya, daga kisan kare-dangi a kasar Myanmar da a baya ake kira Burma.

An yanke shawarar hakan ne duk da cewa jarogar gwamnatin kasar, Aung San Suu Kyi, ta kare kasar ta da kanta kan zarge-zargen a watan jiya.

Dubban ‘yan Rohingya sun mutu, sannan fiye da mutum dubu 700, sun tsere zuwa Bangladesh a lokacin da sojoji suka far masu a 2017.

Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa za a iya sake samun irin wannan kisan kare-dangin.

Karar, wadda kasar Gambiya ta shigar a kotun, ta yi kiran a dauki matakan gaggawa kan sojojin Myanmar har sai an gudanar da cikakken bincike.

Myanmar ta sha dagewa cewa sojojinta na yakin magance masu tsattsauran ra’ayi ne a jihar Rakhine.A takarda da ta fitar na kariya kan karar a babban kotun Hague, Aung San Suu Kyi, ta kwatanta rikicin a matsayin yakin cikin gida da ‘yan ta’addan Rohingya suka kai hare-hare kan wuraren aikin jami’an tsaron gwamnati

Leave a Reply