Home Labaru Zaben Kaduna: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Isah Ashiru Da Jam’iyyar...

Zaben Kaduna: Kotu Ta Yi Watsi Da Karar Isah Ashiru Da Jam’iyyar PDP

752
0
Isa Ashiru Kudan, Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna Na jam’iyyar PDP
Isa Ashiru Kudan, Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna Na jam’iyyar PDP

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamnan jihar Kaduna, ta tabbatar da Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin wanda ya kashe zaben gwamnan jihar.

Yayinda ya ke gabatar da hukuncin, mai shari’a Ibrahim Bako ya bayyana cewa, Isah Ashiru na jam’iyyar PDP ya gaza gabatar da hujjoji a kan zargin da ya ke yi wa Nasir El-Rufai na jam’iyyar APC.

A karar da jam’iyyar PDP da dan takar ta Isah Ashiru su ka shigar dai, sun ce an tafka magudi a zaben gwamnan jihar Kaduna da ya gudana ranar 9 ga Maris na shekara ta 2019, don haka kotu ta kwace kujerar Nasir El-Rufa’i.

Sai dai kotun ta ce, jam’iyyar PDP da Isah Ashiru ba su kawo kwararan hujjojin da ke nuna an tafka magudi ba, don haka jam’iyyar APC da dan takar ta Nasir El-Rufa’i ne su ka lashe zaben.