Home Labaru Atiku Da Buhari: Kotu Na Shirin Yanke Hukunci A Wannan Makon

Atiku Da Buhari: Kotu Na Shirin Yanke Hukunci A Wannan Makon

404
0

Kotun sauraren zaben shugaba kasa za ta yanke hukuci a kan karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar su ka shigar.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 21 ga watan Agusta, mai shari’a Mohammed Garba ya bayyana cewa, za a sanar da dukkan bangarorin da abin ya shafa ranar da za a yanke hukunci.

Kotun zaben dai ba ta sa ranar yanke hukunci ba, amma wa’adin da doka ta tanada zai kare a ranar Asabar, 14 ga watan Satumba na shekara ta 2019.

A na shi bangaren, lauyan hukumar zabe Yunus Ustaz Usman, ya ce hukumar ta gudanar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu daidai da dokar zabe, don haka masu karar ba za su taba iya sauya hakan ba.

Lauyan shugaba Buhari Wole Olanipekun, ya bukaci kotun ta yi watsi da karar saboda rashin hujja, inda ya ce sashe na 131 na kudin tsarin mulkin Nijeriya bai bukaci a sa shahadar cin zabe a ciki takardun ba.

Sai dai lauyan PDP da Atiku Levy Uzoukwu, ya bukaci kotun ta sani cewa sashe na 138 (1) na dokar zabe, ya ce duk dan takarar da ya gabatar da bayanin karya za a soke takarar shi.