Gwamnatin tarayya ta kashe akalla Naira biliyan 1 da miliyan 800 domin ciyar da kananan yara da ke fama da matsananciyar yunwa a jihohi 18 tsakanin shekara ta 2017 da 2018
Shugaban sashen shirin kawar da yunwa na ma’aikatar lafiya Chris Isokpunwu ya sanar da haka, a wata zantawa da ya yi da manema labarai a Abuja.
Isokpunwu, ya ce sakamakon binciken da ma’aikatar lafiya ta gudanar a shekara ta 2017, ya nuna cewa jihohi 18 a kasar nan su na fama da matsananciyar yunwa.
Ya ce a dalilin haka, gwamnati ta tsara matakai tare da hada hannu da Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya, domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Nijeriya.
Isokpunwu ya kara da cewa, a shekara ta 2017, gwamnati ta ware Naira biliyan 1 da miliyan 800, domin samar da kula ga kananan yaran da ke fama da matsananciyar yunwa a jihohin Anambara da Bayelsa da Edo da Bauchi da birnin tarayya Abuja.