Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP Isa Ashiru Kudan, ya ce ya na nan a kan bakan sa na karbo ‘yancin nasarar sa a kotun sauraren kararrakin zabe.
Isa Ashiru dai bai yi na’am da sakamakon zaben da aka yi a jihar Kaduna ba, don haka ya garzaya kotu, ya na mai tabbatar wa Magoya bayan sa cewa yanzu haka su na kotu, kuma za su samu nasara a kan jam’iyyar APC.
Haka kuma, Isah Ashiru Kudan ya yi godiya, tare da jinjina wa magoya bayan sa a kan gudunmuwar da su ke badawa.
Ya ce yanzu haka magana ta fara nisa a gaban kotun sauraren kararrakin zabe, inda ya ke sa ran karbe nasarar da ya samu a zaben, inda ya ce ba zai amince da sakamakon zaben ba, ya na mai ikirarin cewa shi ne ya yi nasara amma jam’iyyar APC ta murde ma shi.