Home Labaru Dambarwa: Gwamnoni Sun Shige Wa Sanata Lawan Gaba A Shugabancin Majalisar Dattawa

Dambarwa: Gwamnoni Sun Shige Wa Sanata Lawan Gaba A Shugabancin Majalisar Dattawa

393
0
Sanata Ahmad Lawan
Sanata Ahmad Lawan

Gwamnonin jam’iyyar APC sun fara gwagwarmaya, domin shige wa Sanata Ahmad Lawan gaba wajen ganin ya zama Shugaban majalisar dattawa.

Wasu daga cikin su sun gana a daren Lahadin da ta gabata a Abuja, dangane da yadda za su karfafa kudirin Sanata Lawan shi ne zabin jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari.

Sanata Lawan ya halarci taron, wanda ake ganin ya na daga cikin matakan da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ke bi gabannin rantsar da majalisar ta 9.

Taron wanda aka fara da misalin karfe 8pm, ya kai har karfe 10:30 na dare. Sai dai ba a bayyana jerin gwamnonin da sauran mutane da su ka halarci tattaunawar ba.

Daya daga cikin wadanda su ka shirya taron, ya ce an sanar da ganawar ne bisa umurnin Shugaba Buhari zuwa ga gwamnoni domin ganin an isar da kudirin Lawan don ganin ci-gaban Nijeriya.

Leave a Reply