Wasu zababbun Sanatocin jam’iyyar APC sun nuna bacin ran su, a kan jawabin da Bola Tinubu ya yi na tilasta masu zaben shugaban majalisar dattawa.
Tuni dai wasu daga cikin zababbun Sanatocin sun gana a Abuja, domin tattaunawa a kan zabin da jam’iyyar APC ta yi da kuma matakin da za su dauka.
Idan dai za a iya tunawa, a karshen makon da ya gabata, Tinubu ya ce duk wanda bai amince da zabin jam’iyyar APC a kan Sanata Ahmad Lawan da Femi Gbajabiamila ba ya fice daga jam’iyyar.
Zababbun
‘yan majalisar sun tuna wa Tinubu cewa, jam’iyyar APC ta kowa da kowa ce ba
mallakar mutum daya ba.