Sama da jami’an zabe 270 ne su ka mutu a kasar Indonisiya, bayan sun tagayyara daga kirga kuri’un miliyoyin ‘yan kasar da su ka jefa.
Rahotanni sun bayyana cewa, akasarin su sun fara rashin lafiya ne sakamakon dogon lokacin da su ka dauka su na kirga kuri’un.
Mai magana da yawun hukumar zabe ta kasar Arief Susanto, ya ce akwai kusan jami’an zabe dubu 1 da 878 da su ka fara rashin lafiya.
Irin wannan dai shi ne zabe na farko a kasar mai mutane kusan miliyan 260, inda aka hada zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da na yankuna.Wata majiya ta ce an hada zabubbukan ne a lokaci guda domin saukakawa gwamnati wajen kashe kudade, amma da alamun hakan ya sa jami’an zaben cikin wahala har wasu su ka rasa rayukan su, inda mai magana da yawun hukumar zaben kasar ya ce tsananin aiki ne ya kashe ma’aikatan zabe 272