Home Labaru Ministan Shari’a Ya Fayyace Matsayin Sa A Kan Albashi Naira 30,000

Ministan Shari’a Ya Fayyace Matsayin Sa A Kan Albashi Naira 30,000

274
0

Ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce babu abin da ya rage wa Ma’aikatu da Hukumomi wajen biyan Naira 30, 000 a matsayin mafi karancin albashin Ma’aikata.

Abubakar Malami ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce ba tare da bata lokaci ba za a fara biyan Ma’aikata mafi karancin albashin da shugaban kasa ya sanya wa hannu.

Ministan ya bayyana haka ne, a daidai lokacin da labarai ke yawo cewa har yanzu ana jiran Ma’aikatar sa ta kammala wasu ayyuka kafin a kara wa Ma’aikata albashi,

Malami ce za a fara biyan albashin ba tare da jiran amincewar komai daga ofishin sa ba, ya na mai cewa da zarar shugaban kasa ya sa kudirin cikin dokar kasa abin da za a jira kwai shi ne karshen wata ya yi.

Ministan ya cigaba da cewa, babu abin da ya shafi ma’aikatar sa da karin albashi, illa kawai Ma’aikatan gwamnati da ke da alhaki su cika umarnin da shugaban kasa ya bada.