Home Labaru Zaben Gwamna: PDP Ta Yi Nasara Kan Zaben 2019 A Kotun Jihar...

Zaben Gwamna: PDP Ta Yi Nasara Kan Zaben 2019 A Kotun Jihar Taraba

269
0

Kotun zaben gwamna ta jihar Taraba ta kori karar da Abubakar Danladi  na jam’iyyar APC ya shigar a gabanta wanda yake kalubalantar sake zaben gwamna Darius Ishaku na jam’iyyar PDP da aka yi.

Alkalai uku ne karkashin jagorancin mai shari’a M.O. Adewara suka yanke wannan hukuncin. Lokacin da suke yanke hukuncin sun tabbatar da cewa wadanda suka shigar da karar sun kasa kawo shaidar da za su tabbatar da abubuwan da suke zargin zaben gwamnan da su.

Kotun ta ce  tun biyo bayan wani hukunci da babban kotun jihar ta yanke ranar 6 Maris, 2019 mai lamba FHC/JAL/CS/01/2019, wanda ya hana Danladi damar tsayawa takara, saboda haka ya zama bas hi daga cikin ‘yan takarar da za a zabe su a wancan lokacin.

Mai sahari’ar ya ce, tun karar ta kai har kotun koli wadda kuma ta yanke hukunci saboda haka APC bat a da dan takara.

Kotun ta ce, ko da kuwa za bi yawan kuri’un da ‘yan takarar suka samu ne, ita jam’iyyar APC ba ta da cikakkiyar shaidar da za tabbatar da hakan,domin kuwa ana tabbatar da zabe da ma fi rainjayen halastacciyar kuri’a.