Home Labaru Zaben Katsina: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Masari A Zaben 2019

Zaben Katsina: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Masari A Zaben 2019

654
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Kotun sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a zaben 2019 da ya gabata.

Kotun wacce alkalai uku suka yi hukunci, an samu rinjayen alqalai biyu kan daya. Inda biyu suka kori karar, daya kuma ta soke zaben gabadayansa.

Mai Shari’a Hadiza Ali Jos ita ce ta ce, ta soke zaben Gwamna Masari saboda bai cancanci zama dan takara ba, kuma ta bada umarni a sake zabe cikin kwana casa’in ba tare da Masari ya shiga zaben ba.

Sai dai kuma mai shari’a E.B Omotoso da kuma mai shari’a A.I Ityonyiman suka ce sun kori wannan kara saboda rashin cancantar karar kuma sun tabbatar da Masari a matsayin gwamnan jihar Katsina.