Home Home Buhari Ya Kaddamar Da Ginin Cibiyar Yaki Da Cututtuka Ta Afirka A...

Buhari Ya Kaddamar Da Ginin Cibiyar Yaki Da Cututtuka Ta Afirka A Abuja

58
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ginin Cibiyar Kula da Lafiya ta Afirka a Abuja.

Cibiyar, wacce za ta kasance muhimmiya a bangaren kiwon lafiya ana sa ran za ta kawo sauyi a fannin kula da lafiya a Yammacin Afirka gaba daya.

Shgaba Buhari ya kaddamar da cibiyar ne a ranar Talatar nan, inda ake sa ran za ta lakume sama da Dalar Amurka Miliyan 300.

Bankin Shige da Fice na Afirka tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da Asibitin Kings College da ke London da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Wisconsin na Amurka da na Christies da ke birnin Manchester ne zasu gudanar da aikin gina cibiyar.

Cibiyar za ta kunshi kwararan gadaje 500, yayinda za ta yi aiki a bangarorin cututtukan daji da na zuciya da kuma cututtuka masu yaduwa.

A karshe ya yaba wa Ma’aikatun Ciniki, Zuba Jari da Masana’antu, da Harkokin Waje da kuma na Lafiya bisa jajircewar su wajen ganin an tabbatar da wannan babban ci gaba.