Home Labaru Zaben Filato: Jam’iyyar APC Ce Ta Yi Nasara A Mazabar Pengana

Zaben Filato: Jam’iyyar APC Ce Ta Yi Nasara A Mazabar Pengana

199
0

‘Dan takarar Jam’iyyar APC Yakubu Yackson,  ne ya lashe zaben mazabar Pengana a majalisar dokokin jihar Filato a zaben da aka shirya, inda ya doke PDP.

Yackson ya kayar da Yakubu Busa-buji na jam’iyyar PDP da ratar kuri’u fiye da 2000, kamar yadda sakamakon zaben da hukumar INEC ya nuna.

Karanta Labaru masu Alaka: Kotu Ta Kwace Kujerar PDP A Majalisar Wakilai Ta Ba Jam’iyyar APC

Yakubu Yackson,  ya sami kuri’u dubu 9 da dari 222 ne a zaben, yayin da Yakubu Busa-buji wanda ya zo na biyu ya sami kuri’u dubu 7 da 83.

Babban jami’in  hukumar  zabe ta kasa Farfesa Noel Wanang daya jami’ar tarayya da ke Jos ne, ya bayyana sakamakon zaben, ya ce ‘dan takarar APC ne ya lashe zaben da aka yi.

Noel Wanang, ya sanar da sakamako ne a madadin hukumar INEC a babbar makarantar gwamnati da ke Jingre a cikin karamar hukumar Bassa ta jihar Filato, inda a ka tattara kuri’un.