Home Labaru Haraji: An Sa Ma Sabani Tsakin Najeriya Da Kamfanin MTN

Haraji: An Sa Ma Sabani Tsakin Najeriya Da Kamfanin MTN

543
0

Kamfanin MTN dake Najeriya, ya  ce sun sami rashin jituwa da gwamnatin tarayya a game da wasu tara da aka ci kamfanin a shekara  ta  2015.

Babban jami’in hulda da yada labarai na kamfanin a Najeriya Onome Okwah, ya yi magana a game da wani jawabi da hukumar karbar harajin Najeriya ta yi kwanaki.

Karanta Labaru Masu Alaka: Kamfanin MTN Ya Biya Naira Biliyan 330

Bayanin kamfanin MTN ya sha ban-ban da na hukumar tattara haraji ta Najeriya, akan kudin da aka ci tara shekaru 4 da su ka wuce.

Onome Okwah, ya ce sun biya hukumar haraji kudi da aka yanke masu, sai dai su na da ja a game da wani kwamitin haraji da shugaban hukumar  tattara haraji ta Najeriya da ministar kudin suka kafa, amma ya ce duk da haka kamfanin  MTN za su ci gaba da bin dokokin harajin Najeriya sau da kafa.

Daga shekara ta  2001, kamfanin ya kashe fiye da tiriliyan 2 domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya, inda aka kashe fiye da tiriliyan 1.7 wajen biyan haraji.

A bangaren hukumar  haraji kuwa shugaban hukumar Babatunde Fowler,  na zargin kamfanin MTN da zaftare haraji daga cikin tarar biliyan 330 da hukumar sadarwa ta ci kamfanin na MTN.