Home Labaru Zaben Bayelsa Da Kogi: INEC Ta Kayyade Lokacin Zaben Fidda Gwani

Zaben Bayelsa Da Kogi: INEC Ta Kayyade Lokacin Zaben Fidda Gwani

564
0

Hukumar Zabe mai zaman kan ta ta Najeriya INEC  ta kayyade wa’adin  fara shirye-shiryen da suka shafi zaben gwamna ga jam’iyyu a jihohin Kogi da Bayelsa, da aka tsara yi a ranar 16 ga watan Nuwamba.

Babban kwamishinan hukumar na kasa har wa yau shugaban kwamitin wayar da kan al’umma kan muhimmancin amsar katin zabe Festus Okoye, ya bayyana haka a karshen wani taron manyan jami’an hukumar da ya gudana a Abuja.

Kan batun zaben fidda gwani na jam’iyyun Festus Okoye, ya ce idan har lokacin da ka kayyade wa jam’iyyun su gudanar da zaben fidda gwanin tare da mika sunayen wadan da suka tsayar ya kare to su sani babu maganar ba wata jam’iyya dama kuma.

Ya ce ana tunatar  da jam’iyyu cewa bisa manhajar  da aka fitar kan zabukan a ranar 16  ga watan mayu kowace jam’iyya za ta kammala shirye-shiryen ta ne zuwa ranar alhamis 5 ga watan satumbar 2019 nan.

Shugaban kwamitin ya cigaba  da cewa ranar kar she ta mika sunayen ‘yan takara da kuma muhimman takardun su a shelkwatar hukumar dake Abuja zai zama litinin 9 ga watan satumba kuma zuwa karfe 6 na yamma.

Ya bukaci jam’iyyu su bada hadin kai kan wa’adin da aka kayyade domin hukumar ba zata lamunci zuwa a makare ko neman kara wa’adi ga jam’iyya ba.

Da ya juyo ga maganar amsar katin zabe kuma ya ce hukumomin zabe na jihohin biyu za su shirya wani taron masu ruwa da tsaki a daukacin kananan hukumomin jihohin daga ranar 26 zuwa 30 ga watan Agusta domin wayar da kai kan muhimmancin amsar katin zabe.
p62a