Home Labaru Tamntance Rahotanni: Sarkin Kano Ya Gargadi ‘Yan Jarida

Tamntance Rahotanni: Sarkin Kano Ya Gargadi ‘Yan Jarida

398
0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II, ya gargadi ‘yan jarida su guji yada rahotanni masu cin rai domin kawai su sayar da jaridun su.

Ya kara da cewa; ya kamata a ce ‘yan jarida su daina bizne hakikanin sakonni ga masu karatunsu ta hanyar yin kanun labari mai daukar hankali wanda ka iya jawo rikici.

Muhammad Sanusi II, ya bayyana hakan ne a garin Kano a lokacin da kungiyar wakilan kafafen yada labarai karkashin kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Kano ta kai masa ziyarar bangirma.

Ya ce manyan mutane da dama na son fadin wani abu dangane da abubuwan dake faruwa a Najeriya amma suna tsoron yadda za a sauya musu zance ya koma wani abu daban.

Sarkin Kanon ya ce Najeriya na fuskantar tarin matsalolin zamantakewa da na tattalin arzikin kasa wanda ya kamata ace an ba gwamnati shawarar yadda za ta magance su.

Ya tunatar da ‘yan jaridar cewa suma fa ‘yan Nijeriya ne dake fuskantar irin matsalolin da sauran al’umma ke fuskanta dan haka akwai bukatar su maida hankali wajen bankado hanyoyin da za a magance matsalolin ba wai kambama su ba.

Ya jinjinawa manema labaran kan irin kokarin da suke yi, sai  ya yi kira a gare su, su ci gaba da gudanar da ayyukan su bisa kwarewa.

Leave a Reply