Home Labaru Zaben Anambra: IGP Ya Takaita Zirga-Zirgar Ababen Hawa Daga Daren Juma’A Zuwa...

Zaben Anambra: IGP Ya Takaita Zirga-Zirgar Ababen Hawa Daga Daren Juma’A Zuwa Asabar

53
0

Gabannin zaben gwamna da za a yi a jihar Anambra, shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Usman Baba Alkali, ya bada umurnin takaita zirga-zirgar ababen hawa a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Frank Mba ya fitar, ya ce dokar dai za ta fara aiki ne daga misalign karfe 11:59 na daren ranar Juma’a, 5 ga watan Nuwamba, zuwa karfe 11:59 na daren ranar Asabar.

Shugaban ‘yan sandan, ya ce matakin zai ba rundunar tsaro damar lura da jihar sosai, wajen tabbatar da tsaro domin dakile safarar ‘yan bangar siyasa da masu tada kayar baya, tare da hana amfani da kananan makamai da miyagun kwayoyi a lokaci da bayan zaben.

Usman Baba Alkali, ya kuma umurci jami’an zabe da masu sa ido da aka tantance, da ‘yan jarida da sauran jami’an da aka ba izini su gudanar da ayyukan su bisa doka a lokacin zaben tare da sanya katin shaidar aikin su.