Home Labaru Kasuwanci Gwamnatin Tarayya Ta Kashe N538M Wajen Zubar Da Tsofaffin Kudi Guda1.51BN

Gwamnatin Tarayya Ta Kashe N538M Wajen Zubar Da Tsofaffin Kudi Guda1.51BN

69
0

A wani rahoton shekara ta 2020 da sashen ayyukan kudi na Babban bankin Nijeriya CBN ya fitar, ya ce an yi watsi da takardun kudi na kimanin Naira Miliyan 698 da dubu 480 a shekara ta 2020.

Babban bankin Nijeriya dai, ya ce ya kan lalata takardun Naira, wadanda su ka yi datti ko su ka yage domin tabbatar da cewa sabbin udade ne su ka fi yawa a hannun mutane.

Wannan dai ya na kunshe ne, a cikin dokar da ta kafa Bankin CBN ta shekara ta 2007, sashe na 18 (d).

Babban Bankin, ya ce a karshen watan Disamba na shekara ta 2020, an zubar da akwatunan kudi guda dubu 151 da 427, sabanin Naira Miliyan 814 da dubu 437 da 60 da aka zubar a shekara ta 2019.

Ya ce adadin akwatuna cike da lalatattun kudin da aka zubar a shekara ta 2020, ya yi kasa da akwatuna dubu 5 da 790 idan aka hada da wadanda aka zubar a shekara ta 2019 sakamakon dokokin kulle na cutar Korona.