Home Labaru ‘Yan Daba Hana Sanata Danjuma Goje Shiga Garin Gombe

‘Yan Daba Hana Sanata Danjuma Goje Shiga Garin Gombe

124
0

Wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne, sun hana Sanata Danjuma Goje shiga garin Gombe, yayin da ya je domin halartar daurin aure, inda ya sauka a filin jiragi na jihar Gombe.

Wata majiya ta ce, ‘yan dabar sun tare babban titin Gombe zuwa Bauchi, kusa da Babban Dakin Taro na kasa da kasa, inda su ka cinna wuta a titin domin hana shiga ko fita daga Gombe.

Majiyar ta ce, an fasa gilashin wasu motocci, yayin da aka kona wasu da dama, sannan mutane da dama sun samu raunuka sakamakon lamarin.

Ta ce matafiya sun yi cirko-cirko a hanyoyin biyu, amma an tura jami’an tsaro su kwantar da tarzomar, duba da cewa akwai matasa a ɓangarorin biyu ɗauke da makamai.

Leave a Reply