Home Labaru Zaben Anambra: Ba Zan Yarda Da Wannan Zaben Ba, Kawai Magudi Akayi

Zaben Anambra: Ba Zan Yarda Da Wannan Zaben Ba, Kawai Magudi Akayi

116
0

Kwamitin yakin zaben Sanata Andy Uba ta yi watsi da sakamakon zaben gwamnan jihar Anambra da hukumar zabe ta kasa watau INEC ta sanar ranar Laraba.

Kwamitin tace babu abinda ya faru a zaben nan illa magudi da rufa-rufa kuma ba haka al’ummar jihar suka so ba.

Ambassador Jerry Ugokwe, a jawabin da ya saki ranar Alhamis a madadin kwamitin ya bayyana cewa Hukumar INEC ta yiwa dan takaran APC, Sanata Andy Uba, murdiya ne kawai.

A cewar kwamitin, mutanen da suka rage a APGA basu wuce Gwamnan jihar Willie Obbiano, Farfesa Charles Soludo da iyalansu ba. 

Leave a Reply