Home Labaru Kasuwanci EFCC Ta Kama Lucky Igbinedion Tsohon Gwamnan Jihar Edo

EFCC Ta Kama Lucky Igbinedion Tsohon Gwamnan Jihar Edo

75
0

Hukumar yaƙi da rashawa ta kasa EFCC, ta tabbatar da kama tsohon Gwamnan Jihar Edo Lucky Igbinedion kan zargin cin hanci.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajuren, ya faɗa wa manema labarai cewa Mista Igbinedion ya je ofishin su na Abuja domin amsa tambayoyi game da ɓatan kuɗi naira biliyan 1.6.

Rahotanni na cewa gwamnatin Edo ce ta karɓi rancen kuɗin ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan amma sai aka gan su a asusun wani kamfani da yake da hannu a ciki.

A 2008 ma, gwamnan wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 ya fuskanci tuhuma daga EFCC, inda har aka ɗaure shi wata shida a gidan yari bayan ya amsa aikata laifi ɗaya daga cikin 191 kan ɓatan naira biliyan 2.9.