Hukumar magance yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 53 ɗauke da cutar korona ranar Alhamis a Najeriya.
Hukumar ta ce kazalika, cutar ta kashe ƙarin mutum 11, abin da ya sa adadin wadanda suka mutu ya zama 2,933.
Jihohin da aka samu Karin wadanda suka kamu da cutar su ne PLagos-19, Abuja-7, Plateau-7, Rivers-7, Imo-5, Kano-4, Zamfara-2, Bayelsa-1, Gombe-1
NCDC ta ce ya zuwa yanzu jumillar mutum dubu 212 da 947 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya, Sai kuma 205,000 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke.
You must log in to post a comment.