Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, ya ce lokaci ya yi da ya dace yankin Kudu maso Gabas su fitar da shugaban kasa a zaben 2023.
Balarabe Musa ya ce dukkannin yankunan Najeriya sun fitar da shugaban kasa, yankin na Kudu maso Gabas ne kadai ya rage inda yunkuri na hana yankin damar fitar da shugaban kasa baya neman zaman lafiya.
Tsohon gwamnan ya ce lokaci ya yi da ya dace a ba yankin damar fitar da dan takaran shugaban kasa a zaben shekara 2023.
Ya ce dukkannin sauran sassan Najeriya sun fitar da shugaban kasa tun da aka dawo mulkin demokradiyya a 1999, amma banda yankin Kudu maso Gabas, saboda haka duk wanda baya son yankin ta fitar da shugaban kasa mutum ne mai son rikici.
Dattijon ya bayanna cewar lokaci da dama suna magana a kan tsarin karba-karba da kishin yanki kuma munyi magana a kan yankun hudu na Najeriya, Arewa, Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu.
You must log in to post a comment.