Home Labaru Ranar ‘Yan Jarida: Yada Labaran Karya Na Kara Tabarbara Harkartsaro

Ranar ‘Yan Jarida: Yada Labaran Karya Na Kara Tabarbara Harkartsaro

335
0

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Bauchi, ta ce yadawa da sakin labarun karya na kara rura wutar rigingimu da ake samu a Najeriya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar dauke da sanya hanun sakataren ta Yakubu Muhammad Lame, domin taya ‘yan jarida murnar zagayowar ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya’ a bana, kungiyar ta ce ana bukatar kowani dan jarida ya kula wajen binciken hakikanin labari kafin ya yada ko wallafawa domin kaucewa sakin labarai marasa tushe.
Sanarwar ta tunatar da ‘yan jarida su sani shi labaran kanzon kurege babbar barazana ce ga aikin jarida, don haka ake bukatar kowani dan jarida ya tafiyar da aikin sa bisa kwarewa.
Ta cigaba da cewa kungiyar a yanzun ta maida hankalinta ne matuka wajen yaki da labaran karya a fadin Najeriya, domin yawaitar labaran karya na haifar da rikice-rikicen addini da na kalibanci.
Yakubu Lame, ya kara da shawartar ‘yan jarida a kowani lokaci su yi bincike tare da tabbatar da sahihancin labari kafin su kai ga yadawa, dan ba wai hanzarin sakewa jama’a labari shine gwaninta ba, a’a tabbatar da sahihancin sa ya fi zama gwaninta.
Sanarwar ta kuma bukaci kafafen watsa labarai su ci gaba da gudanar da aikin su na yi wa jama’a hidima yadda ya kamata ta hanyar rahotonnin su da labaran su domin gina kasa da kuma tabbatar da gwamnatoci suna gudanar da aiyukan da suka dace.
Yace ana bukatar bangarorin tsaro na ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su rika daukar ‘yan jarida a matsayin abokan tafiya domin gina kasa da shawo kan matsalolin da ake yawan samu.
Ita dai ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta duniya majalisar dinkin duniya ce ta ware domin ‘yan jarida su samu hanyoyin magance matsalolin su da kuma tabbatar da suna samun ‘yancin su a fadin duniya.

Leave a Reply