Home Labaru Kiwon Lafiya Ebola: WHO Ta Koka Da Karuwar Rasa Rayuka A Congo

Ebola: WHO Ta Koka Da Karuwar Rasa Rayuka A Congo

398
0

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta nuna fargaba kan karuwar mutanen da su ke mutuwa sandiyyar annobar cutar Ebola a Jamhuriyyar Demokradiyyar bayan mutuwar wani jariri mai watanni 9 da haihuwa.

A cewar hukumar wadda ta fara tunanin sauya maganin rigakafin cutar da ake amfani da shi yanzu haka a kasar ta Congo, adadin wadanda cutar ta hallaka ya kai 994 yayinda zai iya cikewa dubu guda kowanne lokaci daga yanzu.

Hukumar ta WHO ta ce za ta sauya maganin da ta fara amfani da shi na Merck a matsayin rigakafi zuwa wani nau’in magani da kamfanin magani Johnson & Johnson, zai samar.

Sai dai babban dakaraktan hukumar ta WHO Dr Michael Ryan, ya ce akwai yiwuwar a hada magungunan biyu don gaggauta kawar da cutar ta Ebola, da ke cigaba haddasa asarar rayuka a kasar.

A wani taron manema labarai da ya kira a Geneve, Dr Ryan yanzu haka akwai mutane dubu 12 da ke zaman jiran magungunan cutar ta Ebola, dai dai lokacin da matsalar tsaro ke ci gaba da barazana ga aikin agaji a kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Leave a Reply