Home Labarai Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Ce Idanun Duniya Na Kan Jami’an Tsaron...

Zaben 2023: Shugaba Buhari Ya Ce Idanun Duniya Na Kan Jami’an Tsaron Kasa

48
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shaida wa babban sufeton ‘yan sandan Najeriya da manyan hafsoshin soji cewa idon ‘yan Najeriya da ma duniya baki ɗaya na kan su, yayin da yake musu kyakkyawan fata na samar da tsaron da ake buƙata wajen gudanar da babban zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Shugaban ƙasan ya faɗi hakan ne a jawabin da ya gabatar  a shelkwatar tsaron ƙasa da ke nan Abuja, yayin ƙaddamar da kayan aikin tsaro da rundunar ‘yan sanda ta samar.

Shugaba Buhari ya yaba wa Babban sufeton ‘yan sandan Usman Baba Alƙali, game da managartan sauye-sauye da ya kawo wa rundunar ‘yan sandan.

Shugaban kasa yay i kira ga babban sufetan ‘yan sanda, da sauran jami’an tsaro za su yi aiki domin samar da isasshen tsaro musamman a lokacin zaɓe, su san cewa idanun duniya na kan su.

Ya ƙara da cewa su sani ana aiki ne da tsarin dimokraɗiyya wanda dokar ƙasa ta samar, kuma duniya na yi wa ‘yan sanda kallon masu tabbatar da doka da oka a tsarin mulkin dimokradiyya.

A ranar 25 ga watan Fabrairun nan ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokoki na ƙasa, sai kuma zaɓen gwamnoni da za a gabatar ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.