Home Home Buhari Ya Murkushe Boko Haram A Najeriya —Buratai

Buhari Ya Murkushe Boko Haram A Najeriya —Buratai

142
0
Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya Laftanar-Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya, ya ce Shugaba Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa na Nijeriya Laftanar-Janar Yusuf Tukur Buratai mai ritaya, ya ce Shugaba Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP.

Buratai ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce babban kuskure ne mutane su rika tunanin daina jin duriyar kungiyoyin baki daya ke nufin an kawo karshen su.

Ya ce hanyar da za a iya cimma hakan kawai ita ce, idan ‘yan ta’addan sun amince da watsi da mummunan tunanin su, su rungumar tsarin Dimokuradiyya, tare da martaba kundin tsarin mulkin Nijeriya da zaman lafiya.

Janar Buratai ya kara da cewa, tun hawan Buhari mulki ya ke da manufofi da tsare-tsaren kawo karshen ‘yan  ta’addan, da kuma dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya baki daya.

Leave a Reply