Home Labaru Zaben 2023: Matasan Ohanaeze Ndigbo Sun Nemi Alfarmar Atiku Abubakar

Zaben 2023: Matasan Ohanaeze Ndigbo Sun Nemi Alfarmar Atiku Abubakar

329
0
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa
Atiku Abubakar, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Matasan kungiyar Inyamurai ta Ohanaeze Ndigbo, sun roki Atiku Abubakar kada ya fito takarar shugaban kasa a shekara ta 2023, domin su samu damar share fagen tsaida dan takara daga yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban kungiyar Okechukwu Isiguzoro, ya bukaci Atiku Abubakar ya nuna dattako ta hanyar hakura da batun sake tsayawa takara.

Ya ce ya kamata Atiku ya mutunta yarjejeniyar da ke tsakanin arewa da kudu, domin ya na da tabbacin mulki zai koma kudu a zaben shekara ta 2023.

Okechukwu ya kara da cewa, Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo ta duniya na da tabbacin mulki zai koma yankin su, don haka sun roki alfarmar kada Atiku Abubakar ya takura wajen samun tikitin takara a shekara ta 2023.

Ya ce jam’iyyun PDP da APC su mika tikitin su na shugabancin kasa a shekara ta 2023 ga yankin kudu, a matsayin hanyar nuna mutunta yarjejeniyar mulkin karba-karba.