Home Labaru APC Da PDP Sun Yi Musayar Kalamai A Kan Zaben Gwamnan Jihar...

APC Da PDP Sun Yi Musayar Kalamai A Kan Zaben Gwamnan Jihar Kogi

367
0

Diraktan yakin neman zaben gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi Smart Adeyemi, ya yi kira ga Hukumar Yaki da Rashawa ICPC ta sa-ido a kan zaben gwamnan jihar da za a gudanar ranar 16 ga watan Nuwamba.

Adeyemi ya yi kiran ne, yayin wani taron manema labarai da ya kira a Lokoja, inda ya ce ana bukatar hukumomin ICPC da EFCC a lokacin zaben, domin su rika lura da yadda jam’iyyar PDP ke neman amfani da kudi ta sayi kuri’un masu zabe.

Ya ce, binciken da jam’iyyar APC ta yi kan dalilan da ya sa PDP ba ta yakin neman zabe ya nuna cewa, sun tara mukuden kudaden da za su yi amfani da su wajen ba hukumar zabe da alkalai cin hanci bayan sun sha kaye a zaben.

Adeyemi ya cigaba da cewa, ba za su nade hannu su na kallo wasu su kakaba wa al’umma gwamna da sanatan da ba zabin su ba.

Sai dai a na shi bangaren, Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Wada na jam’iyyar PDP Faruk Adejoh, ya bayyana zargin da jam’iyyar APC ta yi a matsayin abin dariya.