Home Labaru Raddi: Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Fashola Ya Aje Aikin Sa

Raddi: Jam’iyyar PDP Ta Bukaci Fashola Ya Aje Aikin Sa

310
0
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje
Babatunde Raji Fashola, Ministan ma’aikatar Lantarki, Da Ayyuka Da Gidaje

Jam’iyyar PDP, ta bukaci ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ya aje aiki, sakamakon tsokacin shi akan halin da titunan Nijeriya ke ciki, inda ya ce titunan Nijeriya ba lalatattu ba ne kamar yadda ake yayatawa.

Nasan wannan zai zamo kanun labaranku amma titunan ba sa cikin mummunan halin da ake fada,” ya sanar da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa a Abuja ranar Laraba.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbodinyan, ya kwatanta ikirarin Fashola amtsayin mummunan kalami.

Bayan Jam’iyyar ta bukaci minista ya ajiye aiki, ta kuma nemi ya ba ‘yan Nijeriya hakuri a kan wannan Magana da ya furta.

A karshe PDP ta bukaci jam’iyyar APC ta daina fakewa da mulkin ta na tsawon shekaru 16 ta gaggauta cika alkawurran da ta yi wa ‘yan Nijeriya.