Home Labaru Zaben 2023: Mai Mala Buni Ya Karyata Rahotannin Da Ake Yadawa

Zaben 2023: Mai Mala Buni Ya Karyata Rahotannin Da Ake Yadawa

280
0

Shugaban jam’iyyar APC na riko kuma gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, ya musanta rahotannin dake nuna cewa jam’iyyar APC na kokarin fitar da shugaban jam’iyyar na kasa daga Arewa maso gabashin Najeriya, inda shugaban kasa zai fito daga kudanci, kana arewa maso yamma ta fitar da mataimakin shugaban kasa.

Gwamna Mai Mala Buni, ya ce har ya zuwa wannan lokacin jam’iyyar bata fara wani shiri na fitar da dan takara ba.

Yace sai dai nan ba da jimawa ba za’a fara wannan shirin, amma a yanzu riga Malam Masallaci ne kawai jama’a ke yi, dan haka babu kanshin gaskiya akan zargin da ake yi na cewar, yana goyon bayan tsayar da jigo a jam’iyyar Bola Ahmad Tinubu, a matsayin dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar.


Gwamna Mai Mala, ya kara da cewa Bola Tinubu, da Bisi Akande, jiga-jigai ne a jam’iyyar APC, don haka duk wani abu da za a yi na jam’iyyar sai an tuntube su.

Ya ce, duk wadanda ke cewar Shugaba Buhari, shi ne matsalar jam’iyyar basu san komai a kan jam’iyar ba.

Da aka tabo batun karba-karba kuwa, Mai Mala Buni, ya ce ba a fara maganar ba sai zuwa gaba, don haka fitar da Shugaban kasa da shugaban jam’iyyar, sai nan gaba za a fara tattauna wadannan batutuwa.