Home Labaru Komawa APC: Yakubu Dogara Ya Yi Karin Haske

Komawa APC: Yakubu Dogara Ya Yi Karin Haske

433
0

Tsohon shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya bayyana dalilan da suka sa ya sake sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC bayan shugaban riko na Jam’iyyar Mai Mala Buni, ya sanar da komawar sa Jam’iyyar.

A wasikar da ya rubutawa Jam’iyyar PDP a mazabar sa ta Bogoro, Dogara, ya ce rugujewar shugabanci a Jihar sa ta Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed, da ya taimakawa samun nasara shine dalilin da ya sa ya bar Jam’iyyar.

Dogara, ya ce ba zai iya bude baki ya yi tambaya kan yadda ake tafiyar da gwamnatin Jihar ba sai a zarge shi da rashin biyayya, wannan na daga cikin abinda ya sa ya fice daga Jam’iyyar.

Tsohon shugaban Majalisar ya ce idan ya nade hannayen sa yaki cewa komai kan yadda al’amura ke tabarbarewa a Jihar Bauchi a karkashin gwamnatin Bala Muhammed, zai zama maci amana, bayan a lokacin gwamna Isa Yuguda, da Mohammed Abubakar, kowa ya ji shi ya na bayyana ra’ayin sa idan yaga ba daidai ba.

Leave a Reply