Home Labaru Dambarwar Siyasa: Majalisar Somalia Ta Tsige Firayi Minista

Dambarwar Siyasa: Majalisar Somalia Ta Tsige Firayi Minista

202
0

Majalisar Dokoki ta kasar Somalia, ta tube Firayin minista Hassan Ali Khaire daga mukamin sa, bayan ta kada kuri’ar rashin amincewa da jagorancin sa saboda gazawa wajen daukar matakan tsaro.

Shugaban Majalisar Dokokin Mohammed Mursal Sheikh Abdirahman ya sanar da daukar matakin, wanda ya samu goyon bayan ‘Yan Majalisu 170, yayin da 8 kawai su ka ki amincewa da shirin.

Rahotanni sun ce daukar matakin na da nasaba da takun-sakar da ake tsakanin shugaban kasa Mohammed Abdullahi Mohammed da Firayin minista Khaire, da kuma shugabannin Yankunan kasar a kan ci-gaba da shirin gudanar da zaben da aka tsara a watan Fabarairu na shekara ta 2021.

Shugaban Majalisar dokokin, ya ce Firayin minista Khaire ya gaza wajen kafa rundunonin tsaron da za su tabbatar da tsaro a matakin Jihohi da kuma tarayya.

Shugaban kasa Mohammed ya sanar ta gidan rediyo cewa, ya amince da matakin da Yan Majalisun suka dauka, kuma nan bada dadewa ba zai nada wani sabo da zai maye gurbin Khaire da aka tsige.