Home Home Zaben 2023: Kwankwaso Ya Ce Kar ‘Yan Najeriya Su Biye Wa...

Zaben 2023: Kwankwaso Ya Ce Kar ‘Yan Najeriya Su Biye Wa PDP Ko APC

77
0
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya kada su biye wa manyan jam’iyyu biyu wato APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaben 2023.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga ’yan Najeriya kada su biye wa manyan jam’iyyu biyu wato APC mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta PDP a  babban zaben 2023.

Tsohon sanatan na Shiyyar Kano ta Tsakiya, ya ce babu abin da manyan jam’iyyun biyu za su yi wa ’yan Najeriya tinkaho da shi da zai janyo ra’ayin su domin zaben su a babban zaben na badi da ke tafe.

A cewar sa, manyan jam’iyyun biyu babu abin da suka tara face mahassadda, yana mai kiran ’yan Najeriya maimako su sake zaben su, su mai da hankali kan wata jam’iyya ta daban domin hakan ne kadai zai kai su zuwa tudun mun tsira.

A baya bayan nan dai ana ci gaba da alakanta Kwankwaso da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa wata jam’iyyar, lamarin da ke kara tsamin dangartaka tsakanin sa da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP a Jihar Kano.