Home Labaru Shigo Da Gurbatattaun Mai: Kungiyoyin Arewa Sun Bukaci Shugaban NNPC Ya Yi...

Shigo Da Gurbatattaun Mai: Kungiyoyin Arewa Sun Bukaci Shugaban NNPC Ya Yi Murabus

58
0
Gamayyar kungiyoyi masu zaman kan su 25 na Arewa ne, suka yi kiran yi wa kamfanin man fetur na Najeriya NNPC garambawul kan gurbatattun man da aka shigo da su daga waje.

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kan su 25 na Arewa ne, suka yi kiran yi wa kamfanin  man fetur na Najeriya NNPC garambawul kan gurbatattun man da aka shigo da su daga waje.

Kungiyar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun shugaban ta da kuma kakakin ta, Malam Ibrahim Bature, da Kwamared Abdulsalam Moh’d Kazeem, sun yi Allah wadai da karancin man fetur da ake fama da shi a fadin Najeriya.

Kungiyar ta bukaci shugaban kamfanin na NNPC Mele Kyari, da wasu daraktoci su gaggauta yin murabus saboda abin da suka kira karya tarihin gwamnatin shugaba Buhari na rashin ganin karancin mai tun hawar sa karagar Mulki.

Makwanni uku da suka gabata ne dai Najeriya ta fada cikin matsalar karancin mai, sakamakon gurbataccen man da aka shigo da shi, lamarin da ya janyo dogayen layuka a gidajen mai.