Home Home Zaben 2023: Inyamuri Ni Ke Son Ya Zama Shugaban Kasa A Shekara...

Zaben 2023: Inyamuri Ni Ke Son Ya Zama Shugaban Kasa A Shekara Ta 2023 – Obasanjo

89
0
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce ba karamin dadi zai ji ba idan dan kabilar Igbo ya zama Shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala a shekara ta 2023.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce ba karamin dadi zai ji ba idan dan kabilar Igbo ya zama Shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala a shekara ta  2023.

Obasanjo, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a hada kan ‘yan Nijeriya, ta hanyar ba dan yankin kudu maso gabas shugabancin kasar nan.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne, yayin da dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Sam Ohuabunwa ya kai ma shi ziyara a gidansa da ke Abeokuta.

Ya ce bayan hadin kan kasa da hakan zai haifar, ya yi imanin cewa hakan zai taimaka wajen samar da arziki da yaki da talaucin da su ka addabi Nijeriya.