Home Home Rusau: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Kwace Takardar Shaidar Digirin El-Rufa’i

Rusau: Kungiyar ASUU Ta Yi Barazanar Kwace Takardar Shaidar Digirin El-Rufa’i

80
0
Kungiyar Malaman jami’o’i reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ta dage a kan cewa sai jami’ar ta kwace takardar shaidar digiri ta gwamnan jihar Kaduna saboda karbe ma ta filaye da kuma rufe katangar ta da ya yi.

Takaddama tsakanin jami’ar da gwamnatin jihar Kaduna a kan filin ta da ke Mando a garin Kaduna dai ta sa gwamnatin jihar rushe katangar jami’ar, lamarin da ya fusata ma’aikata da malamai su ka fara zanga-zanga.

Shugaban kungiyar malamai reshen Jami’ar Ahmadu Bello Dakta Haruna Jibril, ya ce an rusa bangon jami’ar da ke kare dalibai daga wasu matsaloli duk da kotu ta bada umarnin kada a yi.

Malaman dai sun yi kira ga hukumomin Jami’ar su janye digirin El-Rufai saboda abubuwan da ya ke yi ba su dangaci wanda ya ke da shaidar takardar gama jami’ar ba.

Duk da nuna damuwar da jami’ar Ahmadu Bello ta yi dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce ba babu gudu babu ja da baya a kan rushe gine-ginen da ta ce ba a yi su a kan ka’ida ba.