Home Home Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Bude Wuta A Kan Wata Mota, Sun...

Rashin Tsaro: ‘Yan Bindiga Sun Bude Wuta A Kan Wata Mota, Sun Kashe Fasinjoji 5

40
0
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa, an kashe fasinjoji biyar, yayin da wasu uku suka ji munanan raunuka bayan ‘yan bindiga sun bude wuta a kan wata mota a hanyar ‘Yan Tumaki zuwa Danmusa a safiyar Asabar da ta gabata.

Karamar hukumar Danmusa dai ta na daya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro a jihar Katsina, inda ta raba iyaka da dajin Rugu da yankunan Safana da Kankara.

Wani shaida da ya bayyana sunan sa a matsayin Musa, ya ce yawancin fasinjojin sun fito ne daga Benin na jihar Edo, yayin da daya ke dawowa daga Abuja.

Ya ce fasinjojin da lamarin ya shafa ‘yan asalin Gobirawa da Kaigar Malamai ne.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar lamarina, inda ya ce kai wa motar hari ne mintoci kadan bayan bar garin ‘Yantumaki.